Babu kuskure a fadin kalmar Inda Rabba ba Wahala-Sheikh Daurawa

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

fitaccen malamin addinin musuluncin nan sheakh Aminu Ibrahim Daurawa ya goyi bayan fadin kalmar Inda rabbana ba wahala da ake yawan ambatonta a Cikin Shirin nan Mai Dogon zango Mai Suna A Duniya.

Kadaura24 ta rawaito Sheikh Daurawa ya bayyana hakan ne yayin daya amsa tambayoyi bayan kammala karatun al’adabul mufrad.

Shehun Malamin yace shi a fahimtarsa Babu laifi a Fadi kalmar ta Inda rabbana ba wahala ,Inda yace bayani ne da sharadi Kuma hakan yayi dai-dai.

” Inda rabba rabbana ba wahala ai hakan ya kamata Dana a fada ma’ana an yarda duk Wanda yake tare da Allah ba Zai Sha wahala ba, tabbas Babu laifi a Fadi Wannan maganar”inji Sheikh Daurawa

Babban malamin addinin musulincin nan kuma tsohon shugaban hukumar hisbah ta jahar kano ya goyi bayan su abale da kanabaro, yadda suke fadar wata kalma mai cike da jan jankali.

Kamar yadda kowa yasani jarumin da a yanzu babu jarumin da tauraruwarsa take haskawa mu samman ma tacikin fina finai masu dogwan zango daddy hikkima wanda akafi sani da abale shida Mai gidan sa tijjjani asase wanda akafi sani da kanabaro.

Al’umma da yawa sun dade suna maida martani akan Kalmar saboda yadda ta zamo babu yara babu babba yadda suke fadar Kalmar Sakamakon wani Rubutu da Wani Malami yayi a Kafafen sada Zumunta.

132 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Amfani da al’ada a cikin fina-finan kannywood ne ya hana masa’antar ci gaba – Khadija Osi

Jaruma a masana'antar Kannywood Khadija Muhammad wacce aka fi...

Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi...

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa...

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...