Matakin dakatar da Abba Kyari izina ce ga ƴan sanda – CP Muhammad Wakil
Tsohon Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano CP Muhammad Wakil ritaya ya ce dakatar da DCP Abba Kyari da kuma kaddamar da bincike kan zargin da ake yi masa da hukumar kula da aikin dansanda ta yi shi ne matakin da ya fi dacewa a dauka don sanin gaskiyar lamarin.
A jiya ne dai Hukumar ta dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda sakamakon zargin hannu a wata damfara da Hukumar Binciken Manyan Laifukka ta Amurka FBI ke yi masa.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan ta ɗauki matakin dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ne, bayan shawarar da babban sufeto janar Usman Alkali Baba ya bayar.
Kan haka ne Yusuf Ibrahim Yakasai ya fara da tambayar CP Muhammad Wakili, kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya a Najeriya, wanda aka sani da Singham ko mene ne mataki na gaba bayan dakatarwar?