Mun kwashe tifa sama 1000 ta shara cikin sati 4 a Kano- Dr Kabiru Getso

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kwashe tifa sama da dubu daya ta shara cikin makonni hudu.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci karkare Shirin gangamin yashe Magudanan ruwa na shekarar 2021 a yankin Unguwar Yahaya Gusau cikin karamar hukumar Birni da kewaye.

Dakta Kabiru Getso ya ce an yashe manyan Magudanan ruwa sama da 10 da guraren da suke Tara ruwa sama da 10 ciki harda Kwarin-gogau da Jakara da Shataletalen Triumph da Shataletalen Baban-gwari da ma sauran guraren da dama a cikin kwaryar birnin Kano.

Kwamishinann Muhalli Dr Kabir Getso tare da yan tawagarsa suke duba yadda aikin kwashe shara ke gudana a kano

Ya ce har yanzu baa sami rahoton ambaliyar ruwa ba tunda daminar bana ta fadi inda ya kara da cewa Shiri “Makon tsaftar Muhalli na shekarar 2021” da gangamin yashe Magudanan ruwa na shekarar 2021 sun sami matukar nasarar kula da lafiya da dukiyoyin alumma.

Kwamishinan Muhallin ya ce la’akari da nasarorin da aka samu, Gwamnatin zata tabbatar an kwashe dukkanin guraren zuba sharar da ake dasu a cikin loko da sako na kwaryar birnin Kano.

“Kamar Yadda kuke gani, ina tabbatar wa al’ummar jihar Kano nasarar da muke samu zata cigaba, laakari da irin kokarin da kamfanin da muka saka hanu dashi ya ke yi, kuma muna tabbatar muku cewa sai mun tabbatar Babu bola a jihar Kano, kokarin mu kenan, fatan mu kenan”.

Dangane da wayar da kan al’umma game da dena zubar da shara a Magudanan ruwa kuwa, kwamishinan ya ce maaikatar ta tura kudirin doka ga majalisar dokoki ta jihar Kano Kuma matukar kudirin ya zama doka ya tanadi hukunci ga duk masu zuba shara a Magudanan ruwa da masu gini akan Magudanan ruwa.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya yabawa hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA da hukumar kula da gyaran tituna ta jiha KARMA da sauran Kamfani dangane da gudun mowar da suke bawa maaikatar Muhalli domin samun nasara inda ya bukaci sauran da su yi koyi.

Wakilin Kadaura24 ya rawaito Kwamishinan ya kuma yabawa Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da irin kulawar da ya ke bawa maaikatar ta hanyar sahale dukkan abin da ta ke bukata domin samun nasarar ayyukan ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...