Muna Gab da Fara gyaran Kananan Asibitoci a Kano – Ganduje

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan gaba kadan zata fara gyaran asibitocin dake karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jiha.

Shugaban Hukumar Kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano Dakta Tijjani Hussain ne ya bayyana hakan lokacin Mika lambar girmamawa ga kungiyar tallafawa marayu da masu karamin karfi CSADI dangane da irin gudun mowar da ta bayar wajen horar da mata kananan sana’o’i wanda gidauniyar kula da lafiya mata wato “Clinton Health access Iniatitives” hadin gwiwa da Hukumar kula da kasashe ta kasar Canada suka shirya a Karamar hukumar Dawakin Kudu da ke nan Kano.

Shirin koyar da sana’o’in Wanda mata sama da 110 da suka fito daga kananan hukumomi 11 an gudanar da shi ne domin bunkasa rayuwar Yan mata matasa da ke kananan hukumomi da ake gudanar da Shirin.

Da ya Mika lambar yabo ga kungiyar CSADI shugaban Hukumar Dakta Tijjani Hussain ya ce Gwamnatin jihar Kano ta na daukar dukkan matakai na koyawa mata da matasa sana’o’in dogaro da kai don cigaban rayuwarsu.

“Maaikatar mata da maaikatar matasa harma da hukumar kula da lafiya a matakin farko suna gudanar da harkokin koyawa mata da matasa, idan zaka iya tunawa Mai girma Mai dakin gwamnan Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje da zagaya kananan hukumomin jihar Kano 44 inda aka koyawa mata sana’o’i Kuma aka basu jari”.

A jawabinta, shugabar kungiyar tallafawa marayu da masu karamin karfi CSADI Hajiya Zainab Ahmad Suleiman MFR, JF ta ce abin farin ciki ne yadda kungiyar ta tallafa wajen canza rayuwar mata a yankunan karkara.

Hajiya Zainab Ahmad Suleiman ta ce bayan koya musu sana’o’in, CSADI ta koya musu hanyoyin da zasu rika Tara ribar da suke samu domin inganta jarin su.

“Dole in godewa shugaban Hukumar Kula da lafiya a matakin farko Dr Tijjani Hussain domin da gudu mowarsa ne alumma suka yadda damu a Cikin Shiri, zan kuma godewa CHAI sakamakon bamu kudin da zamu dauki nauyin koyawa matan sana’o’i domin tun daga kasar Canada aka zo aka dubamu Kuma sun gamsu da yadda mukayi aiki, bazan manta da maaikatana na CSADI ba harma da Yan jaridu” Inji Zainab.

Shugabar kungiyar ta Kuma bukaci gwamnatoci da mawadata da su rika tallafawa masu kananan sana’o’i Wanda hakan zai basu damar dogaro da kansu da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Nusaiba Nuhu Adam daga karamar hukumar Kiru da Fatima Abdullahi daga Kumbotso sun yabawa Kungiyar ta CSADI da Kungiyar CHAI bisa rawar da suka taka na canza rayuwar su inda suka ce sana’o’in da suka koya na taka matukar rawa wajen kula da ilimi da lafiya da kuma rayuwarsu baki daya.

Wakilin Kadaura24 ya rawaito mana cewa Kananan hukumomin da aka gudanar da Shirin koyar da sana’o’in dai sun hada da Gabasawa da Garko da Makoda da Rimin-Gado da Shanono da Karaye da Takai da Kiru da Garin-Malam da Kumbotso da kuma Karamar hukumar Ungoggo.

225 COMMENTS

  1. Бій Усик – Джошуа за звання чемпіона світу за версією WBA, WBO та IBF відбудеться в Лондоні. Місцем його проведення стане стадіон футбольного клубу “Тоттенгем”. Щодо дати проведення бою, то Энтони Джошуа Александр Усик Британця турбує той факт, що українець є лівшею. Чемпіон WBA, IBF, WBO і IBO в суперважкій вазі Ентоні Джошуа (24-1, 22 КО) назвав головну перевагу свого опонента в майбутньому поєдинку – українця Олександра Усика (18-0, 13 KO

  2. Про бій Усик – Джошуа оголошено офіційно Александр Усик Энтони Джошуа смотреть онлайн Британця турбує той факт, що українець є лівшею. Чемпіон WBA, IBF, WBO і IBO в суперважкій вазі Ентоні Джошуа (24-1, 22 КО) назвав головну перевагу свого опонента в майбутньому поєдинку – українця Олександра Усика (18-0, 13 KO

  3. Porn, Disenchant dotty Porn Videos, Porno Coitus Tube & XXX Pornography. Motorized Porn Movies – Suffer to in error Iphone Also bush, Android XXX. Subcontract outdoors dippy Porn Movies, Shagging Cinema, XXX Porno Videos & Matured Porn
    free porn video

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...