Abdulmumini Kofa Zai biyawa Dalibai Dubu 2 kudin jarrabawar Neco

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

Tsohon Dan majalissar tarayya mai wakiltar kananan hukomomin Kiru da Bebeji Kuma Babban Darakta a Hukumar Gidaje ta Kasa, Jagoran Jam’iyyar APC na Kiru da Bebeji Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi alkawarin biyawa Dalibai Dubu 2 kudin jarrabawar Neco.

Abdulmumini kofa ya bayyana hakan ne lokacin daya karbi bakuncin shugabancin Dalibai na Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji, Waɗanda suka Kai masa ziyarar girmamawa tare da bukatar ya biyawa Dalibai kudin jarrabawar ta Neco.

Hon Kofa Wanda shi ne jarman Bebeji yayi alkawarin biyawa dukkanin wadannan Dalibai sannan yayi alkawarin samun Maigirma Gwamna domin ya shaida Masa abinda yake shirin yi, sannan zai Sami Hukumar NECO domin ya rokesu su bashi dama ya biyawa wadannan Dalibai.

Kafin nan Hon Kofa ya ziyarci Garin Bebeji domin Mika musu Filin makabartar da ya siya musu, bayan koken da suka kai Masa na cikar Makabartar da suke amfani da ita sama da shekara ashirin, a Karkashin Jagorancin Sarkin Bebeji tare da bukatar siyan wasu gonaki kimanin goma Sha shida. Kofa ya biya Milyoyin Nairori kudin wannan gonaki Kuma akalla za’a kai shekara Hamsin ana amfani da wannan sabon filin.

Shugaban Hukumar Samar da Gidajen ya Kuma ziyarci asibitin Kofa domin duba marasa lafiya saboda bullar cutar Cholera a karamar Hukumar Bebeji, Kafin zuwan sa Hon Kofa ya aika magunguna na Milyoyin Nairori.

Kadaura24 ta rawaito Yayin ziyarar ya bayar da kudin abinci ga marasa lafiya tare da yin Ihsani ga ma’aikatan asibitin domin Kara karfin guiwa.

145 COMMENTS

  1. Джошуа-Усик: объявлен состав пар андеркарда AnthonyJoshua Усик вирушив до Лондона на бій із Джошуа. Усик видел самое неприятное поражение Джошуа в карьере. Тогда он понял, что британец будет чемпионом. Усик зі своєю командою відправився до Лондону

  2. Усик не стал. И не станет. Ему роль такую прописали – помогать нести яйца. Джошуа несёт яйца. И в данном бою он должен снести яйцо с помощью Усика. А потом повтороно – ещё одно яйцо. Ну, принято Энтони Джошуа Александр Усик смотреть онлайн «В этом бое просто нет смысла: Джошуа нокаутирует Усика» – МК

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...