Nada Sarkin Kano Aminu zai zama silar hade kan Arewa-Abdulaziz Yari

Date:

Daga Nusaiba Sani Darma

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar ya bayyana nada Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a Matsayin Sarkin Kano da cewa hanyace ta dinke Arewacin Nigeria.

Alh. Abdulaziz Yari ya bayyana hakan ne Yayin da yake ganawa da Manema labaran gidan gwamnatin jihar Kano.

Abdulaziz Yari yace sarkin Kano mutum ne da yake son cigaban al’ummar yankin Arewa Kuma yake Kaunar Zaman lafiya a Koda yaushe.

“Na zo kano ne domin taya Dan uwana Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Murnar Bikin bashi Sanda da za’a yi Ranar Asabar a Matsayin Sarkin Kano na 15 a Sarakunan fulani” inji Yari

” Ina taya al’ummar jihar Kano dana Arewacin Kasar nan Murnar Wannan Lokaci Kuma Ina fatan za’a yi bukukuwan Cikin kwanciyar hankali da lumana .”Inji shi

Kadaura24 ta rawaito Yari ya Kuma yi fatan al’ummar Kano Zasu cigaba da baiwa Sarkin hadin Kai domin ya Sami damar yiwa al’umma adalci da Kawo Cigaba.

105 COMMENTS

  1. Усик – Джошуа: появились промо JoshuaUsyk Бій Усик – Джошуа за звання чемпіона світу за версією WBA, WBO та IBF відбудеться в Лондоні. Місцем його проведення стане стадіон футбольного клубу “Тоттенгем”. Щодо дати проведення бою, то

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...