Ganduje, NNPC sun sa Hannu Kan yarjejeniyar AKK-Gas

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) da Gwamnatin Jihar Kano sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a kan amfani da Gas dangane da aikin Shimfida Bututun Iskar Gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano.


 Da yake jawabi a ranar Juma’a bayan sanya hannu kan yarjejeniyar a gidan Gwamnatin Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda Mataimakinsa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya bayyana taron a matsayin babban cigaba wajen farfado da tattalin arziki musamman na masana’antu, kasancewar Kano cibiyar  kasuwancin yankin arewacin kasar nan.


 Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labarai na Mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge ya aikowa Kadaura24 ta ce, Dr.Gawuna, ya bukaci masu zuba jari da su yi amfani da damar da Kamfanin NNPC-AKK ya bayar idan an kammala Aikin don bunkasa tattalin arzikin Kano da Kasa Baki daya.


A cewar Gwamnan… wannan aikin yana da matukar mahimmanci a gare mu, a zahiri mun fara ganin sakamako mai kyau Saboda jajircewar kwamitin nan, ina kira gare su da su cigaba da wayar da kan sauran masu ruwa da tsaki game da tasirin aikin saboda Kano tana da girma ta fuskar kasuwa.


 Ya kuma ba da tabbacin cigaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga AKK don ganin aikin ya tabbata.


 A nasa jawabin Manajan Daraktan Kamfanin na NNPC, Mele Kyari wanda Babban Jami’in Gudanar da Gas da Power Engr Yusuf Usman ya wakilta ya bayyana cewa  Shugaba Muhammad Buhari na matukar son daga darajar rayuwar mutanen Kasar nan ta Hanyar Samar da Aikin bututun AKK-Gas Wanda aka hakkake cewa zai  bunkasa tattalin arzikin kasar, ” in ji sanarwar.


 Ya Kara da cewa muna sane da irin tasirin da bututun Iskar Gas ya yi wajen farfado da masana’antu a Legas da kuma yadda a yau ake amfani da shi wajen samar da makamashi ga masana’antun da ke samar da iskar gas don samar da takin zamani da yawa, mun fahimci cewa Kano tana da dimbin karfin gaske ta fuskar kasuwanci Saboda irin matakan da ake Dauka na bunkasa tattalin arzikinta. ” inji Gawuna


Shugaban Kwamitin na nan Kano Injiniya Mu’azu Magaji na Daga Cikin masu ruwa da tsakin da suka halarci sanya hannu kan yarjejeniyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...