Buhari ya kafa kwamitin rage talauci a Nigeria

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da kwamiti na musamman don rage talauci a tsakanin yan kasar da kuma bijiro da dabarun bunkasa tattalin arziki.

A cikin rahotonsa na baya-bayan nan, Bankin Duniya ya ce hauhawar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na kara talaucin da kuma tabarbarewar harkokin kasuwanci.

Bankin ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 7 ne suka fada cikin talauci a shekarar 2020 saboda tashin farashin kawai.

A wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban, ya fitar a ranar Talata, an bayyana mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kwamitin.

BBC Hausa ta rawaito Buhari ya sake nanata alkawarinsa na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru goma, tare da kyakkyawan tsarin bincike don aiwatarwa da kuma samar da kudade.

85 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...