Sheikh Gumi yace da Sanin Gwamnati yake Zuwa Wajen ‘Yan Bindiga

Date:

Malamin Musuluncin nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar tsaro ta DSS ta gayyata ko ta kama shi domin amsa wasu tambayoyi game da alaƙarsa da ‘yan fashin daji.

Shehin malamin ya faɗa wa BBC Hausa cewa “da ma muna da alaƙa” a lokacin da aka tambaye shi ko da gaske ya amsa gayyatar jami’an tsaron.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi

“Babu wanda ya gayyace ni”, in ji shi. Sai dai tun farko mai magana da yawun DSS, Peter Afunaya, ya faɗa wa Channels TV cewa “mun gayyaci malamin domin amsa tambayoyi”.

Da yake magana da Channels, Sheikh Gumi ya ce: “Tun sanda na fara shiga daji, ina shiga ne da jami’an tsaro; tare da sanin ‘yan sanda da DSS da sarakunan gargajiya da shugabannin Fulani. Ban taɓa shiga ni kaɗi ba.”

Kazalika malamin wanda ya sha nema wa ‘yan fashin daji afuwa, ya jaddada cewa bai taɓa zargin rundunar sojan Najeriya ba baki ɗayanta da taimaka wa ‘yan bindigar da suka addabi jihohin arewa.

Haka nan, an san malamin da shiga dazukan da ke arewacin Najeriya domin yin abin da ya kira wa’azi da faɗakar da ‘yan fashin da ke kashe mutane kusan kullum da kuma kama wasu domin karɓar kuɗin fansa.

63 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...