An Gurfanar da Wata Mata da ake Zargi da Kashe Kishiyar ta a Kotu

Date:

Daga Nusaiba Aliyu Salga

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano a ranar Alhamis ta gurfanar da wata mai suna Fadima Dahiru mazauniyar Unguwar Farawa da ke karamar Hukumar Kumbotso a gaban kotu a kan zargin kashe kishiyar ta Mai Suna Waseela har lahira.
 Da take gurfanar da wacce ake kara a gaban Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, Lauya mai shigar da kara Barista Khadija Umar daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta yi zargin cewa Fadima Dahiru a ranar 6 ga Mayu, 2019 da misalin karfe 15:30Hrs ta yi amfani da abu mai kaifi tare da raunata Waseela Wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta har lahira nan take.


 “Kin aikata wani laifi wanda yake karkashin hurumin wannan Kotun mai alfarma da Wanda ya haddasa kisa waseela”.


 Khadija Umar ya fadawa kotun cewa laifin da ake karar  Fatima a Kansa ya sabawa sashi na 221 (A) na pinal code.


 Lauyan da ke kare wadda ake tuhuma Barista Bashir Abdullahi Sufi ya roki kotun da ta ba da damar sauraren karar a rana mai zuwa, mai shari’a Zuwaira Yusuf ta karbi rokon kuma, ta dage sauraron karar zuwa 22 ga Yuli, 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...