Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

Bayan samun nasarar cin jarabawa da kuma da cika duk wasu sharudda da Hukumar Kula da Shari’a ta gindaya Mai girma Babban Alkalin Alkalan Jihar Kano Nura Sagir Umar ya amince da nadin karin Alkalan Kotun Shari’a 34 a bangaren Shari’a na Jihar Kano.
Wannan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa Mai dauke da sa hannun Mai Magana da yawun kotunan Jihar Kano Baba Jibo Ibrahim wadda kuma aka rabawa kaffefe yada labarai har da Kadaura24.
Sanarwar ta ce Dukkanin sabbin Alkalan Kotun Shari’a da aka nada ana sa ran za a rantsar da su a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, 2021 a dakin taro na Babbar Kotun Shari’a dake Kano da karfe 10: am