Sojoji Sun kwato Wasu daga Cikin Daliban Kebbi da aka sace

Date:

Bayanan da ke fitowa daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa sojoji sun kuɓutar da wasu daga cikin yara ‘yan makarantar Gwamnatin Tarayya ta garin Birnin Yawuri da aka sace.

Rahotannin sun ce sojojin sun yi wa ɓarayin ƙofar rago ne a ranar Alhamis da daddare a cikin daji.

Ɗan majalisa mai wakilar Yawuri a majalisar dokokin Kebbi Honorabul Muhammad Bello Ngaski ya tabbatar wa da BBC Hausa labarin.

A ranar Alhamis da rana ne ƴan bindigar suka kutsa makarantar tare da sace yaran.

Wasu shaidu sun shaida wa BBC cewa sun ga gawar ɓarayin dajin fiye da 80.

Shaidun sun ce an yi gumurzu sosai tsakanin dakarun tsaro da ɓarayin dajin a ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar Kebbin.

Sun ƙara da da cewa sojojin sun katse wa ɓarayin hanzari ne ta hanyar yi musu kwanton ɓauna a hanyar tafiya da yaran da suka sata zuwa maɓoyarsu.

“Abin da ya faru a garin Makoko wanda su ɓarayin suka mai da daji, sojoji sun tare su suka yi artabu. Yanzu haka maganar da nake maka an tara gawa sama da mutum 80 na ɓarayin.

“Su kuma yaran yanzu haka akwai kusan bakwai da tabbas sun dawo an anso su. Sannan sojojin sun zagaye dajin da ɓarayin suke, don tun jiya aka tare musu hanyoyin don haka sun kasa gaba sun kasa baya,” in ji wani ganau.

Akwai tazara sosai tsakanin wajen da lamarin ya faru da kuma birnin Yawuri da ak sace yaran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...