Ranar Damokaradiyya : Zaman lafiya shi ne Ginshikin Dunkulewar Nig – Ganduje

Date:

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce zaman lafiya da Hadin kai sune mabuɗin don tabbatar da Hadin kan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ba.


 Ganduje ya bayyana hakan ne a biki da akayi a Kano domin bikin ranar Dimokiradiyya bana.
 Ya bukaci shugabannin dukkan kabilun da su tattauna da juna domin lalubu hanyoyin da za a samu zaman lafiya da hadin kai a kasar nan.


 Gwamnan ya kuma Kara da cewa gwamnonin Kasar nan sun yanke shawarar yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya don kawo mafita mai dorewa game da matsalar rashin tsaro a kasar.


 Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ya ga dacewar karrama marigayi MKO Abiola da lambar girmamawa tare da  girmama shi ta Hanyar Mayar bikin ranar Dimokradiyya ranar 12 ga Yuni.


 “Muna maraba sosai da wannan abin rana, wannan ita ce Ranar Dimokiradiyya.  Muna godiya ga Shugaba Buhari da ya ba Abiola lambar girmamawa bayan mutuntawa ”.


 “Muna aiki tare don tabbatar da cewa an kawar da rashin tsaro a kasar, Muna farin cikin cewa sabbin shugabannin hafsoshin suna kara himmatuww ga wannan aiki, kuma na tabbata Shugaba Muhammadu Buhari yana ba su dukkan goyon bayan da suke bukata. ”


 Gwamnan ya kuma nuna farin cikinsa da matsayin kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo saboda yin imani da tabbatuwar kaswata Najeriya Matsayin Kasa Daya.


 “Matsayin da kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta dauka ya karyata duk jita-jita,  da fargabar barkewar Najeriya kamar yadda wasu marasa kishin kasa suka nuna a tsakanin yan kabilar Ibo”. Inji Ganduje 


Yayin taron an karbi Wasu Yan jam’iyyar PDP Kwankwasiyya da Sauran Wasu da dama da suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC.


 Bikin ya samu halartar Shugabanin da masu Ruwa da tsaki a jam’iyyar APC Sannan da Jami’an Gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

67 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...