An Dakatar da Sarkin Zurmi bisa zargin Haɗa Kai da Yan Bindiga

Date:

Daga khalifa Abdullahi Maikano

Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Mai Martaba Sarkin Zurmi a Jihar Zamfara, Alhaji Atiku Abubakar bisa zargin sa da hannu a karuwar hare-haren ‘yan bindiga a masarautarsa.


 Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Zamfara Alhaji Kabiru Balarabe Wadda kuma aka rabawa manema labarai a Gusau.


 Sanarwar ta ce, an kafa wani kwamiti na mutum 9 da zai binciki zargin a karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ibrahim Wakkala Muhammad da sauran manyan jami’an gwamnati ciki har da wakilan hukumomin tsaro.


 A cewar sanarwar, ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa a cikin makonni 3.


 A halin yanzu, Alhaju Bello Suleiman (Bunun kanwa) shine zai kula da lamuran masarautar da gaggawa

91 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...