Za’a fara ƙera wayoyi na zamani da layuka a Najeriya – Pantami

Date:

Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami ya ce Nigeria na da damar da za ta samar da layukan wayar salula wato SIM card da kuma wayoyin hannu na zamani (Smart Phones) don kasuwancinsu a nahiyar Afirka.

Pantami ya bayyana haka ne yayin wani taro da wata majalisar ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ta shirya a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin labarai na Nan ya ruwaito.

Majalisar ta shirya taron ne ga ministocin gwamnati domin bayyana ayyukan da suke gudanarwa a ofisoshinsu.

Da yake jawabi a wurin taron, Pantami ya ce nan gaba kaɗan za a daina shigar da kashi 60 zuwa 70 na kayayyakin da ake amfani da su a ɓangaren sadarwa zuwa Najeriya daga ƙasashen waje.

Ya ce ƙasar na da ƙarfin da za ta iya samar da layin waya miliyan 200 a duk shekara.

“Mun samar da wani tsari na ƙera aƙalla kashi 60 zuwa 70 na abubuwan da muke buƙata a ɓangaren sadarwa nan da shekara biyu ko uku saboda za mu fara ƙera su a cikin gida, kuma har mun fara,” in ji shi.

“Lokacin da gwamnatin nan ta hau mulki, hatta layukan salula sai an shigo da su daga ƙasar waje. Yanzu gwamnati ta samar da yanayin da ake iya samar da su da kuma ƙera wayar salula ta zamani ba wai kawai don amfanin cikin gida ba, har da nahiyar Afika.

“Yanzu haka a Najeriya, muna ƙera wayoyin salula na zamani.”

267 COMMENTS

  1. Энтони Джошуа и Александр Усик прошли процедуру взвешивания перед боем, который состоится 25 сентября. Прямой эфир на телеканале Рен-ТВ. Вес: Александр Усик — 100,2 кг; Энтони Джошуа — 108,9 кг ПРЯМАЯ ССЫЛКА НА ВИДЕО В этом JoshuaUsyk Усик улетел на бой с Джошуа Украинец Александр Усик (18-0, 13 КО) улетел на поединок с чемпионом мира по версиям wbo, wba, ibf и ibo Энтони Джошуа (24-1, 22 КО). Об этом сообщил… Усик и Джошуа провели битву взглядов Последняя встреча

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...