Zamu Zamanantar da Harkar Sufuri a Kano -Mahmoud Santsi

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada kudurin ta na zamanantar tare da inganta harkar sufuri a jihar nan.

Kwamishinan Gidaje da Sufuri na jihar Honorabul Mahmud Muhammad Santsi ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe wani biki na kwana 2 na taron Kwamitin Kwamishinonin Sufuri na Nijeriya wanda aka gudanar daga 24-25th Mayu, 2021 a Cibiyar Taron Kasa da Kasa dake Abuja.

Ya kara jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar inganta zamantar tare da inganta harkar sufuri ta hanyar samar da kyawawan manufofi, ya kara da cewa a cikin shekaru 2 da suka gabata gwamnatin na aiki ba tare da gajiyawa ba don samun nasarar zamantar da bada lasisin ta Na’ura Mai kwakwalwa da dai sauransu .

Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Ma’aikatar Sufuri ta Kano Yusuf Abubakar Ibrahim ya aikowa Kadaura24 yace Honorabul Santsi ya bayyana cewa, Kwamitin Kwamishinonin Sufurin ya yi alkawarin kawo hadin kai da cikin tafiyar da manufofin dorewar harkokin sufuri a kasar nan, tare da alkawarin yin aiki don samar da dokokin da Gwamnatin Tarayya za ta yi wanda kowa zai bi.

A nasa jawabin, Daraktan Sashin Kula Lafiyar ababen hawa ta jihar Kano, Garba Abdu Gaya wanda ya raka Kwamishinan ya kara da cewa taron yace an gudanar da taron ne domin chanza yanayin aiki daga tsohon tsarin zuwa Sabon tsari irin na Zamani.

A karshen taron an gudanar da zaben sabbin shugabannin zartarwa inda aka zabi Hajiya Ramatu’Yar Adua daga shiyyar Arewa ta Tsakiya a matsayin Shugaba, Dakta Frederick Oladeinde an zabe shi a matsayin Sakatare daga shiyyar Kudu maso Yamma yayin da aka zabi Honarabul Mahmud Muhammad Santsi Ma’aji daga Shiyyar Arewa maso yamma.

14 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...