Daga Nurain Abubakar
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya ce dole ne Fulani makiyaya da ke shigowa jihar su samu izini daga rundunar‘ yan sandan ta jihar Kano.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron gaggawa Kan al’amuran tsaro tare da shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa a ranar Larabar nan, CP Dikko ya ce duk wani Bafulatani makiyayi da ya shigo Kano ba tare da izinin ba za a mai dashi Inda ya fito.
Ya ce wannan shawarar na daga cikin tsare-tsaren tsaro da rundunarsa ta yi a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
“A taron da na yi a ofishina da safiyar yau tare da shugabannin Fulani daga Kaduna, Katsina da Jigawa, na nemi su ba mu duk wani bayani da zasu bamu damar hana duk wanda zai shigo ba tare da izini na dole ba shigowa” . Inji CP Dikko
“Dole ne a samu wata wasikar izini, wanda ke nuna cewa za su zo Kano daga wannan jihar. Don haka, duk wanda ya zo kano ba tare da izini ba daga tsarin ’yan sandanmu daga jihar da suka zo ba, ba shakka za a tsayar da shi a juya shi zuwa inda ya fito.
“Ba za mu yarda da duk wanda zai zo jihar nan ba bisa doka ba. Wataƙila ba mutanen Kirki ba ne, Suna iya zama masu laifi. Suna iya zama ‘yan fashi ko wasu mugayen mutane. Don haka, ba za mu yarda da Haka a nan Kano ba, ”kwamishinan ya jaddada.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da aniyar rundunar na samar da cikakken tsaro ga dukkan ‘yan kasa da kuma baki da ke zaune a jihar kano.
Ya ce rundunar tana aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba wajen tabbatar da hadin kai da sauran hukumomin tsaro a Kano don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Kwamishinan yans mai bayyana cewa sun tsara dabarun tsaro don tabbatar da tsaro ga baƙin da ke gudanar da harkokin kasuwancinsu a cikin jihar.
Ya lura cewa kasancewar Kano cibiyar cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya yana da sama da baƙi 5,000 da ke zaune a jihar don kasuwanci da sauran batutuwan da suka shafi hakan.
Sama’ila Dikko ya kuma ce nan ba da dadewa ba rundunar za ta fara cafke Mutanen da ke kera da kuma sayar da muggan makamai kamar su adda, takobi da wukake ga ‘yan daba.
Ya yi gargadin cewa ana iya tuhumar duk wani maƙeri da aka samu yana sayar da makaman da suke taimakawa ɓarayi.
CP Dikko ya kara da cewa rundunar ta kammala shirye-shiryen fadada sashen ta na Anti-Daba da nufin rage ayyukan barayi a jihar