Wasu Mutane Daga Zamfara na kwararowa K/H Gwarzo – Hon. Kutama

Date:

Daga Surayya Abdullah Tukuntawa

Karamar hukumar Gwarzo ta yi gargadi game da kwararar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba daga jihar Zamfara zuwa yankin ta na ayyukan hakar ma’adinai.


  Shugaban karamar hukumar Bashir Abdullahi Kutama ya yi wannan gargadin ne a wani taron tattaunawa da wakilan hukumomin tsaro, shugabannin kauyuka, limamai, kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.


 Cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun karamar hukumar Rabiu Khalil ya fitar a ranar Alhamis din nan ta ce an gudanar da taron ne don Nemo hanyoyin ingantawa da karfafa tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.


 Shugaban Karamar Hukumar wanda ya gabatar da bakin haure da ke zaune a yankin, ya umarci shugabanni masu rike da sarautun gargajiya da su kafa kungiyoyin tsaro a cikin yankunansu.
 Shima da yake jawabi Hakimin Gwarzo Shehu Kabiru Bayero (Barde Kerarriya) ya roki mutanen yankin da su yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a karamar hukumar ta Gwarzo, Kano da Najeriya Baki daya.


 A nasu jawaban daban, wakilin ‘yan sanda, DSS, NSCDC, da NDLEA sun yaba da alkawurran da shugaban karamar hukumar ya yi a kan al’amuran tsaro kuma sun bukaci mutane su kai rahoton wadanda ba su yarda da su ba ga jami’an tsaro mafi kusa.

149 COMMENTS

  1. Джошуа и Усик провели открытую тренировку. Уже в эту субботу на стадионе «Тоттенхэм» в Лондоне нас ждет грандиозный бой чемпиона IBF, WBA и WBO в супертяжелом весе Энтони Джошуа (24-1, 22 KO) против Джошуа Усик смотреть онлайн Антъни Джошуа ще заработи 17,5 млн. евро за боя с Александър Усик в събота на стадион „Тотнъм” в Лондон, разкриха британският таблоид „Мирър”. Сумата е с 50 процента повече от

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...