Sojojin Najeriya sun kai wani samame wani masallaci da ke Filin Lazio unguwar Hotoro cikin birnin Kano kuma sun kama kimanin mutane 10 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a yammacin Asabar din data gabata.
Shaidun gani da ido sun shaidawa Solacebase cewa aikin wanda bai wuce awa daya ba ya gudana yayin da al’ummar musulmin yankibke gudanar da buda baki.
Lamarin ya haifar da firgici da tsoro ga mazauna yankin, yayin da Sojoji Kuma suka gudanar da bincike a wasu gidaje .
Solacebase ta rawaito cewa nan da nan bayan aikin, Wasu Daga Cikin al’ummar yankin suka kauracewa unguwar Saboda tunanin sojojin zasu iya komawa unguwar.
Lokacin da Majiyar Kadaura24 ta tuntube kakakin rundunar a nanKano Kyaftin Irabor ya yi alkawarin idan ya kammala tattara bayanan Zai sanar da Manema labarai a Ranar Lahadi nan.