Kansila ya Rabawa Mutane 117 Kayan Sallah a Kano

Date:

Daga Rabi’u Usman

Zababben Kansilan Mazabar Na’ibawa Hon Hamza M Abdulkareem ya Rarraba Kayan Abincin Azumin Watan Ramadana da Kayan Sallah harma da Kudaden Cefane ga Al’ummar da yake Jagoranta a yankin Mazabar Na’ibawa da Kewayen ta a Karamar Hukumar Kumbotso.

Yana Mai Cewar, ya Gabatar da Wannan Tallafin ne a Matsayin Somin Tabi ga Al’ummar tasa Sakamakon Basu Dade da Hawa Karagar Mulkin ba, amma nan gaba Za Suyi Abin da yafi hakan da Zarar Komai ya Daidaita.

Ya Kara da cewa, Wadanda Basu Samu Damar Karba a Wannan Lokacin ba, Suyi Hakuri nan gaba Zasu Samu da Yardar Allah, Tunda yanzu aka Fara.

Da Suke Mika Sakon Godiya Wasu Daga Cikin Jama’ar da Suka Amfana da Samun Wannan Tallafin Musamman Iyayen Yara Marayu da Marasa Karfi Sun Bayyana Cewar, Sunji Dadin Wannan Kaya da aka Basu Daidai Lokacin da Suke tsaka da Bukatar Su, Kuma yanzu Suka Samu Shugaba Nagari, Domin kuwa Basu taba Samun Kansilan da yayi Musu Irin Wannan Abin Alkhairin ba a Tarihin Wannan Mazabar ta Na’ibawa.

67 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...