Gwamnatin Tarayya ta gano Masu Daukar Nauyin Ta’addanci a Kasar nan

Date:

Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu wasu fitattun ‘yan Najeriya da kuma ‘yan kasuwar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

Ministan ya ce tuni aka fara shirin gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin fuskantar shari’a akan rawar da su ke takawa wajen haifar da tashin hankali sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar a Daular Larabawa dangane da masu daukar nauyin bai wa boko haram kudade.

Wannan matsayi na gwamnati na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar karuwar hare haren ayyukan ta’addanci na boko haram a yankin arewa maso gabas da kuma wasu hare haren na daban a wasu yankuna.

Malami ya ce gwamnati ta dauki dogon lokaci ta na gudanar da bincike akan wannan lamarin da ya shafi ayyukan ta’addanci bayan da kotu a Daular Larabawa ta daure wasu ‘yan Najeriyar guda 6.

Ministan ya ce binciken da suka dauki dogon lokaci su na yi ya nuna musu wasu mutane da hukumomi da ke da hannu wajen jefa kasar cikin tashin hankali.

RFI ta rawaito cewa Malami ya ce suna da kwararan shaidun da ke nuna musu irin wadannan mutanen da ke daukar nauyin baiwa ‘yan ta’adda kudade kuma yanzu kotu ce za ta tabbatar da wannan zargi.

73 COMMENTS

  1. To allah y kara baku sa a akan abunda kaka sa a gaba su kuma nasu aikata irin wannan laifi allah ya kara tona asirinsu Allah ya kara dauka ka kasa ta Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...