Sakamakon Tattaunawar Majalisar Dattawa da Shugabannin tsaro

Date:

Shugabannin tsaron Najeriya da na ‘yan Majalisar Dattijan Najeriya sun yi wata tattaunawar sirri a zauren majalisar dokokin kasar da ke Abuja.

Hafsoshin tsaron sun amsa gayyatar ‘yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.

Daga ƴan majalisar har shugabannin tsaron ba su ba da cikakken bayani kan abubuwan da suka tattauna ba amma a wani saƙo da majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce sun tattauna ne kan batutuwan tsaro da suka haɗa da fashin daji da ta da ƙayar baya da ta’addanci da kuma hanyoyin kawo ƙarshensu a Najeriya

Sai dai Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin soji a majalisar ya bayyana wa BBC cewa wannan ce tattaunawa mafi armashi da Majalisar Dattawan ta taɓa yi da shugabannin tsaroWannan tattaunawa ta yi armashi kuma mun fahimci juna sosai da shugabannin tsaron,” a cewarsa.

“Za mu ba da goyon baya a ba su dukkan abun da suke buƙata don su kawo ƙarshen waɗannan matsalolin tsaro,” in ji Ndume.

Sai dai ya ce ba zai bayyana ainihin abin da suka tattauna ba saboda sirri ne, ya ce akwai batutuwan da ba za a iya ambatowa ba.

Ya kuma ce majalisar ta gamsu da bayanan da shugabannin tsaron suka yi masu kuma za su taimaka masu da abubuwan da suke buƙata.

Sanata Ndume ya ce akwai abubuwan da shugabannin tsaron suka bayyana wa majalisa da ba su taɓa sani ba dagane da matsalar tsaro a Najeriya.

“Bayanan sirri ne da ba zan iya faɗa ba amma a wannan tattaunawa mun yi masu tambayoyin da ba mu taɓa yi masu ba, kuma su ma sun ba mu amsoshin da ba mu sani ba,” in ji Ndume.

Ali Ndume ya ce mataki na gaba da za ɗauka shi ne duba ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi sannan a ware wa shugabannin tsaro kuɗin da suke buƙata don yin aiki yadda ya kamata.

Sauran jami’an da ke amsa gayyatar sun haɗa da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na shugaban hukumar tsaron farin kaya wato DSS.

Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ƙasa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ƙarfe 11:21.

Suna wannan ganawa ne a yayin da Najeriya take ci gaba da fama da matsalolin tsaro daga kowacce kusurwa ta ƙasar.

A arewa maso yammacin kasar ana ci gaba da fama da matsalolin masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji, wadanda suke kashe mutane ko kuma su tilasta musu biyan kudin fansa.

Wannan matsala ta fi ƙamari a jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da kuma Katsina.

Alƙaluma sun nuna cewa an sace ɗalibai fiye da 800 daga watan Disamba zuwa yanzu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...