Daga Rabi’u Usman
Biyo Bayan Kaddamar da Littafin da Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta yi, Wanda Za’a Dinga Wallafa Bayanan Dukkannin Masu Karbar Hayar Gidaje Ko kango da Filaye keyi a lungu da Sako a Fadin Jihar Kano Dama Kasa Baki Daya, Shugaban Kungiyar Masu Hada Hadar Filaye da Gidaje da Mamallaka Gidajen Haya na Kasa Alhaji Musa Khalil Hotoro ya Goyi Bayan Wannan Kudirin na Jami’an Yan Sanda Domin Samar da Ingantaccen tsaro a Jihar Nan dama Kas Baki Daya.
Yana Mai Jan Kunne da Gargadin Mambobin Kungiyar Su dasu Kasance Masu Baiwa Jami’an Yan Sanda Cikakken Hadin Kai Wajen Samar da tsaro a Duk inda Suke Domin tsarkake Harkokin Dillancin Su.
Musa Khalil ya lashi Takobin Gurfanar da duk Wanda Suka Kama Dan Kungiya da Karya Dokar Gwamnati da Kuma ta Jami’an tsaro a Gaban Shari’ah.
A Karshe yayi Kira ga Al’umma dasu Kasance Masu Taimakawa Jami’an Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Wajen Bayar da Bayanan Sirri da Zarar Sunga Motsin Abin da Basu Amince da Shi ba.