Ramadan :Gwamnatin Kano ta Baiwa Dalibai tallafin Azumi

Date:

Daga Rabi’u Usman

Shugaban Hukumar Bayar da Tallafin Karatu na Jihar Kano (Kano State Scholarship Board) Mudassir Umar Bebeji ya Bukaci Daukacin Daliban Jihar Kano dasu Baiwa Sabon Zababben Shugaban Dalibai yan Asalin Jihar Nan Hadin Kai da Goyon Baya Wajen Ciyar da Daliban gaba ta Fannoni Daban Daban.

Mudassir Bebeji ya Fadi Hakan Ne yayin da yake Bude Sabuwar Sakatariyar Ofishin Dalibai na yan Asalin Jihar Kano dake Kan Titin Zuwa Jami’ar Bayero a Nan Kano.

Yana Mai Cewar, ta Haka ne Za’a Samar da Shugabanci na Gari ga Dalibai a Jihar Kano da Kuma Samar da Tagomashin da Gwamnatin Jihar Kano Ke Bayarwa ga Dalibai na Bayar da Tallafin Karatu da Samar da Guraben Karatu a Kasashen Ketare, Wanda a Wannan Karon aka Baiwa Daliban Shinkafa da Kudi Domin Cigaba da Gudanar da Azumin Watan Ramadana Mai Falala.

Da yake Jawabi a Madadin Dalibai yan Asalin Jihar Kano, Shugaban Daliban Comrade Hamza Musa Uba ya Jaddada Godiya ga Kafatanin Daliban Makarantu Daban Daban na Kananan Hukumomi 44 da Suka Samu Halartar Gagarumin Taron da aka Gudanar a Wannan Rana a Harabar Ofishin Hukumar Bayar da Tallafin Karatu na Jihar Kano (Kano State Scholarship Board), daga Nan ya lashi Takobin Gudanar da Shugabanci Na Gari.

Wakilin Kadaura24 ya Ruwaito Mana Cewar, daga Cikin Wadanda Suka Halarci Taron Bikin Bude Katafariyar Sakatariyar Kungiyar Dalibai yan Asalin Jihar Kano Sun Hadar da Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa Hon Auwal Aranfosu da na Karamar Hukumar Birni da Kewaye Hon Fa’izu Al-Findiki da Masu Taimakawa Gwamnan Kano akan Harkokin Dalibai.

67 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...