Rahotonni sun tabbatar da cewa fitaccen dan ta’addan da ya shirya sace ‘Yan Makarantar Kankara a cikin jihar Katsina, Auwalun Daudawa an kashe shi.
Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan ya koma daji.
Kwamishanan tsaron harkokin cikin gida na jihar Zamfara, Abubakar Justice Dauran ne ya tabbatar wa DW Hausa da labarin.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe Daudawa ne da yammacin ranar Juma’a a lokacin da sukai musayar wuta da wasu gungun abokan hamayyarsu a dajin Dumburum da ke tsakanin karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara da karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.
Shahararren dan fashin nan ya yi kaurin suna bayan da ya kitsa kai hari a Makarantun Sakandaren Gwamnati da ke Kankara inda ya sace sama da ’yan makaranta 300 a cikin dare.
Watanni biyu bayan haka, dan fashin ya bayyana a Gusau, babban birnin Zamfara, tare da mutanensa biyar inda ya sanar da tubansa tare da mika bindigogin AK guda 20 da wasu makamai ga ‘yan sanda.
Really enjoy Kadaura 24. May Allah guide you in all your effort.
Lallai Kadaura na bayar da gagarumar gudunmawa ga makaranta Hausa a Jafar sadarwa zamani.
Allah ya taimaki Kadaura.