Dan Majalisa Lado Suleja Ya Kaddamar Da Rabon kudi Naira Miliyan Hamsin Ga Jama’ar Sa.
A Safiyar Talata Ne Dan Majalisar Kasa Dake Wakiltar Suleja Tafa Da Gurara Hon Lado Suleja Ya Rabawa Mutane Dari Da Ashirin Tsabar Kudi Naira Miliyan Hamsin.
Dan Majalisa Wanda Yace Bayan Salla Da Mako Daya Za’a Cigaba Da Rabon kudin Inda Mutane Dari Biyu Da Arba’in Zasu Samu Naira Miliyan Dari, Ya Kalubalenci Wadanda Suka Ci Gajiyar Kudin Da Suyi Amfani Dashi Yadda Yakamata.
Wadanda Suka Ci Gajiyar Sun Samu Naira Miliyan Daya-Daya Da Kuma Wasu Sun Samu Naira Dubu Dari Biyar-Biyar.
Allah yai jagora amin ya bada ikon sauke nauyin alumma