Kano tayi datti, muna bukatar hanzari wajen magance matsalar sharar -Gwamna Ganduje

Date:


Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 Gwamnan jihar Kano Umar Abdullahi Ganduje ya yi tir da yanayin kazantar da jihar ke ciki a yunkurin gwamnatinsa na Kara daga darajar jihar Kano zuwa babban birnin a Duniya. 


 Gwamnan ya bayyana yayain taron Majalisar Zartarwa ta Wannan makon , inda yayin Zaman Majalisar wani kamfani ya ganatar d Kudirinsu na hada hannu da gwamnatin Jihar domin magance matsalar shara a Kano.


Ganduje yace hakan yanayin rashin kula da shara, kalubalen da yake haifarwa da kuma bukatar samar da mafita mai dorewa don ci gaban birnin na Kano.


Gwamna Ganduje ya ce jihar na ta yin shawarwari kan shirin cutar da jihar Kano gaba domin birnin yayi gogayya da sauran birane, amma kalubalen kula da shara yana kawo cikas ga burin hakan.


 Ya ce illar rashin kyakkyawan kulawa da shara ya mamaye ko’ina a Kano, wanda ke haifar da mummunan yanayi na lafiya kamar su cutar kansa da ire-iren matsalolin kiwon lafiya, lamarin da ke jawo wa gwamnati makudan kudade.


Gwamna Ganduje yace gwamnatin zata hada hannu da kamfanoni Masu Zaman kansu domin Kawo Karshen matsalar shara ta Hanyoyi daban-daban don cigaban Kano

113 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...