Ganduje ya yiwa Sarakunan Kano da Bichi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsu

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana rasuwar Hajiya Maryam, Mai Babban Dakin Kano kuma matar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a matsayin babban Rashi ba ga al’ummar Jihar Kano ba kadai har da Kasa baki daya.

Ya nuna juyayinsa a madadin gwamnati da jama’ar jihar Kano ga Sarakunan Kano da Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero Daya bayan daya.

A cikin sakon ta’aziyya da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan, wanda ya kara bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai ladabi da gaskiya mai tarbiyantar da yayanta kan tafarkin Allah, ya yi wa sarakuna ta’aziyyar Rasuwar mahaifiyarsu.

Ganduje ya ce mutuwar ta a wannan lokacin ta haifar da wani yanayi mai wahalar cikewa musamman ga ‘ya’yan ta maza guda biyu wadanda ke matukar bukatar jagora da shawarwari daga uwa.

Gwamnan ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya sanya marigayir a Aljannah Firdausi da kuma karfin gwiwa ga dangin, da daukacin mutanen da ke Masarautar guda biyu don jure wannan babban rashi.

80 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...