December 9, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Zamu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Sayar Da Biskit Mai Dauke Da Kayan Maye – Buba Marwa

Shugaban Hukumar hana fatauci da shan miyagun kwayoyi, NDLEA, Burgediya Janaral Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya gargadi masu kantuna (Supermarket), da su gaggauta kawar da biskit mai dauke da sinadarin maye a shagunan su da rubun ajiyan su.

Idan baku manta ba dai, hukumar ta NDLEA a makon nan ta kama wani matashi da budurwar sa suna sarrafa biskit wanda suke sayarwa yaran makaranta a makarantu da dama a fadin Nijeriya. Bincike ya nuna duk wanda ya ci wannan biskit na musamman yana fita hayyacin sa a cikin kankanin lokaci saboda sinadarin bugarwa dake ciki.

Marwa yayi gargadin ne lokacin da yake karban rahoton aiki daga kwamandan hukumar NDLEA reshen shiyar birnin tarayya Abuja, dangane da kama dalibar aji uku a jami’a mai suna Rhoda Agboje tare da saurayin ta Ifeanyi Nwankwo, wadanda suka kware wajen sayar da biskit mai dauke da Kwaya ga yaran makaranta, kantunan sayar da abu da wuraren shakatawa a Abuja.

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa Shugaban na hukumar ta NDLEA yace zasu dauki mataki akan manyan kantuna, wuraren shakatawa sauran su, tare da masu mallakan su, wadanda suke sayar da alawa ko makamantan sa wanda aka surka da kwaya.

Yace baza su bari masu sarrafa irin wadannan abu su kai ga baiwa yara kanana da ma manya a cikib al’umma ba. “baza mu yi kasa a guiwa ba sai mun ga mun dakile wannan haramtaccen kasuwanci irin nasu. Saboda haka ina amfani da wannan daman, ina gargadin masu shaguna da kanti, da su yi gaggawa tsabtace ma’adanan su da shagunan su daga miyagun sinadarai da aka sarrafa su cikin wani nau’i na abinci” inji Janaral Marwa.