Yan Bindiga suna son kure Hakuri na akan su – Shugaba Buhari

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan cewa “Su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba”.

Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da ‘yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara.

Shugaban wanda ya yi gargadin cewa “Za a kawo karshen Irin wannan rashin girmama rayuwar mutanen da ‘yan bindigar ke yi a kusa ba da dadewa ba”, ya kara da cewa, “Dole mu dakatar da wannan kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba”,

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da al’ummar jihar Zamfara cewa “duk da gazawar da muka yi a kokarinmu na kare ‘yan kasarmu, ba za mu taba bayar da kai bori ya hau ba wajen murkushe wadannan marassa tausayin.”

Buhari ya yi alkawarin kaddamar da wani shirin soji na musamman a Zamfara domin “dakile hare-haren ‘yan bingidar” da kullum ke kamari.

“Gwamnatinmu ba za ta yarda da kai kashe ‘yan kauyen da ke talakawa ba suke fama da talauci da sauran matsalolin rayuwa,” in ji Buhari a wata sanarwa da kakainsa ya fitar Garba Shehu

71 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...