Mun gamsu da irin Abincin da ake rabawa Masu Azumi a Kano – Muhd Garba

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

Gwamnatin Jihar Kano tace tana gaisuwa  da yadda aikin dafawa da rabar da abincin buda bakin azumin Ramadan na wannan shekara yake gudana. 

Jagoran duba yadda ake dafawa da rabar da abincin buda bakin na jihar Kano Wanda kuma shine Kwamshinan Yada Labarai na Jihar Malam Muhammad Garba shine ya bayyana hakan a wani rangadin bazata da Kwamitin yakai wasu cibiyoyin dafa abincin na musamman.

Cibiyoyin kuwa sun hadar da Babban Masallacin Juma’a na Sheikh Ahmadu Tijjani dake kofar Mata da Kwalejin Fasaha ta Kano da kuma Hotoro Tsamiyar Boka.

Kwamitin ya yabawa masu aikin dafa abincin bisa yadda suke tabbatar da sunbi dukkanin ka’idojin dafa abinci inda suke cika mazubin zuba Abincin domin wadatar wadanda suke amfanarsa.

Jami’In kula da kafafan yada labarai na Kwamitin kuma Babban mai Taimakawa Gwamna ba Musamman akan kafofin yada Labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa yace Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Ja’afar Ahmad Gwarzo ya gargadi masu aiki dafa abincin su dunga tabbatarwa suna bin dokokin tsaftace muhallin da suke aikin girka abincin.

Wasu daga cikin mazauna unguwannin da kwamitin ya zagaya sun yabawa Gwamnatin Jiha bisa samar da abincin ciyarwar azumin watan Ramadan kyauta a kowace rana.

 Malam Haladu mai Itace ya ce ya dogara da ciyarwa kyauta domin yin buda baki da zarar ansha ruwa.

 Haladu ya ce yawan abincin da ake bayarwa ya ishe shi buda baki kullum kuma yakan ajiye a wasu lokutan domin yin sahur.

 Ita ma Zainab Garba wacce bazawara ce a Hotoro Tsamiyar Boka, ta ce ciyarwar abincin buda bakin kyauta da Gwamnatin Jihar Kano keyi tabbas yana taimaka Mata  wajen ciyar da ’ya’yanta Marayu guda shida da mai gidanta ya mutu ya bar Mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...