Daga Kamal Yahaya Zakaria
Kasa da mako guda da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ziyarci jihar Bauchi, kodinetan jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Dr Babayo Liman da daruruwan magoya bayansa sun fice daga NNPP zuwa jam’iyyar PDP a jihar.
Da suke ganawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), a Bauchi, sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Liman ya ce Atiku Abubakar ya na da kwarewa da gogewar da zai ceto kasar nan daga halin kunci da tabarbarewar tattalin arzikin da take ciki idan aka yi la’akari da abubuwan da ya yi a baya a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru takwas.

Ya ce, “Na zo nan ne domin in sanar da manema labarai da sauran jama’a cewa a yau ni Babayo Liman na yi murabus daga mukamina na sakataren shiyya na NNPP kuma dan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, sannan ko’odineta na Kwankwasiyya, na fice daga jam’iyyar na koma jam’iyyar PDP.
“Anan ina tare da wasu shugabannin zartarwa na NNPP da dubban magoya bayana domin bayyana aniyar mu ta komawa jam’iyyar PDP da kuma goyon bayan takarar Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya da Bala Mohammed a matsayin gwamnan jihar Bauchi .
“Ina kira ga dukkan magoya bayana a yankin Arewa maso Gabas da su bi matakina na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, sannan kuma ina kira ga magoya bayana a jihar Bauchi da su yi hakan don ceto kasata Nigeria.”