Gwamnatin tarayya zata karawa Ma’aikatan ta Albashi – Chris Ngige

Date:

 

 

Ministan ƙwadagon tarayyar Nigeria Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati a ƙasar domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a ƙasar.

 

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Villa.

Talla

 

Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasar ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata a ƙasar, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa.

 

 

Da aka tambaye shi sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, sai ministan ya ce ”ƙwarai kuwa, wannan shi ne abin da nake faɗa cewa kwamitin albashi da shugaban ƙasar ya kafa na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumar albashin ma’aikata ta ƙasar”.

 

“Dan haka yayin da muka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ƙarin albashin”, in ji ministan.

 

Kan batun albashin wata takwas da malaman jami’o’in ƙasar ke buƙatar gwamnati ta biya su kuwa, Ministan ya ce batun na gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...