Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Guda cikin yan jam’iyyar APC a jihar kano Hon. Anas Abba Dala ya bayyana cewa al’ummar arewacin Nigeria sun tsayar da matsayar mara baya ga Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.
Anas Abba Dala ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a kano .
Yace al’ummar arewacin kasar nan wadanda suka hadar da masu kudi, talakawa, yan kasuwa da yan boko sun hadu sun yanke shawarar Marawa Atiku Abubakar bayan saboda shi ne suka gamsu yana da manufofin da su tallafawa yankin.

- ” Abubuwan da suke faruwa na yadda al’ummar arewa ciki har da yan jam’iyyata ta APC suke nunawa a wurare daban-daban sun tabbatar da matsayar da muka dauka na marawa Atiku Abubakar baya, kowa ya Kalli abun da ya faruwa a jihar Katsina yadda akaje taron dan takarar gwamnan jihar, amma idan aka ce Nigeria sai a ce sai Atiku l, wannan babbar hujja ce”. A cewar Anas Abba Dala
Anas Abba Dala wanda yake ikirarin cewa shi dan jam’iyyar APC ne ya bayyana cewa jam’iyyar sa ta gaza wajen fitar da al’umma daga cikin mawuyacin halin da suke ciki, ga Kuma matsalar tsaro data fi addabar kowa a kasa.
Hon. Anas Abba Dala ya kara da cewa hakan tasa yake kira ga daukacin al’ummar Nigeria da su fito ranar zabe domin zabar Jam’iyyar PDP a zaben Shugaban Kasa ko sa sami sassaucin halin da suke ciki.