Daga Kwamared Al-Ameen Albarra
Dakatarwar da akayiwa Hon. Sha’aban Sharada, Hon. Alimi, da Hon. Adewale a APC,haramtacciya ce saboda an karya dokoki 5.
Aranar 17, 18 dakuma 21 ga watan shida na 2021 muka ga manyan jaridun Nigeria sun rawaito labarin cewa jam’iyar APC ta dakatar Hon. Barrister Kolapo Alimi, har na tsawon watanni 12 a jihar Osun, mazabar Elerin “c” abisa zargin yiwa APC zagon kasa.
Haka suma jam’iyar PDP, a jihar Lagos, sun dakatar da tsahon shugaban jam’iyar na jihar maisuna Hon. Segun Adewale, amma na tsawon wata daya bisa zargin yiwa jam’iyar zagon kasa.
Kazalika a jihar Kano ma jam’iyar Apc ta dakatar da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, har na tsawon wata 12. Kuma an dakatar dashi ne bisa zargin yiwa jam’iyar kafar Angulu, daga bisani suma wasu bangare na shugabannin jam’iyar APC suka fusata da wannan hukuncin inda suka kori Sani Fata Sharada, daga shugabancin APC ta karamar hukumar burnin Kano.
Matsayin mu na manazartana alkaluman siyasa da harkokin mulki, duka! wadannan dakatarwa guda hudu haramtatu ne, dai-dai suke da babu, domun sun saba ka’idojin kundin tsarin mulkin Nigeria sashi na 35 da na 223 na kwaskwararren kundin tsarin mulki na 1999,cewa anshiga hakki kuma an tauye damar da doka ta baiwa kowanne dan kasa, haka . Haka Kuma kundin tsarin mulkin jam’iyar su ta APC, Shashi na 9, 11 da sashi 21. ya bayyana sharuda yadda ya kamata a Kori Dan jam’iyya Kamar haka :Farkodai dole ne sai zababbun Shugabanin jam’iyya ne suke da ikon yin kwamati sai a gaiyaci wanda ake zarki ta hanyar wadda take tabbatacciya wato sako na rubuce ko kuma na baka da baka banda kila-wakala wato na yanar gizo, a tabbata shi ne bawani ba, sai asheda masa cewa ana gaiyyatar ka kazo ga laifukan da ake zargin ka aikata, zo ka kare kanka, idan anbashi damar kare kansa agaban daukacin shugabanni jam’iyar to sai sai kuma ansamu biyu bisa uku na shugabanni cewa sun yarda laifun ya tabbata sabo da haka adakatar dashi. to dole ne sai anbi wannan Dole ne fa sai anbi dukkan ka’idojin shi ne zai zama dakatarwa ta yuwu, amma a haka gaskiya anyi aikin wofi! Kuma duk wanda suka kaucewa waddannan ka’idojin zai rasa fa’ida domun sun aikatawa kundin tsarin mulki jam’iyyar su zububi Babban. Babu shakka idan Waɗanda aka Dakatar din suka Kai kara kotu Akwai kyakykyawan zaton zasu Nasara akan jam’iyyar Saboda basu bi doka ba,Kotu zata iya soke waddannan dakatarwa bakidanya kuma kotunma zata iya cinsu tara ma.
Wannan shi ake kira gudu aduhu, bulayi bara akufai, idan aka duba asalin wannan rigima san zuciyane da rshin daukar qaddara, tundaga zaban kujerar majalisar tarayya wadda SHA’ABAN IBRAHIM SHARADA yake kai wannan rigima take ta ruruwa, wanda hakan saida suka je kotun koli, mulki Allah ne ke bada shi ga wanda yaso,
HON MUNTARI ISHAQ YAKASAI shi Allah ya bawa jagorancin kano municipal kuma Allah ya bashi kujerar kimishina,
Idan muka duba wannan mutane zamuga duka Allah ya basu dama ta kera ta yanda kowa zai ciyar da jama’ar wannan yanki gaba wato kano municipal,
Amma wadannan shugabannin sunki su gane haka sai yaqar juna suke suna koyawa jama’ar yankina rigima da gaba, hakan yasa ni IBRAHIM AHMAD ADAM (KHALIL 77 ) nai tur da Allah wadai da wannan shuganaci nasu, domin suna komar da yankina baya, da koya musu tarbiyyar rikici mara amfani, daga qarshe bada kowa suke fadaba da Allah suke fada, kuma basu gode da ni’imar da Allah ya basu ba, wajan bawa kowa abinda ya dace dashi ba,
Zamani da lokaci zaiyi aiki akan su cikin yardar Allah nan bada dadewa ba
Hmmmm kasata kenan!wato shi dima ma Kujerar da yake yi bai karya kaida ba Sai korar sa da akayi?
Koda basu Dakatar Dashi ba Wllhi muyi shiri tsaf Domin muga bai Kuma Samun sahalewar komawa wannan matsayin ba, Domin Ai se mun bar kannen mu da iyayen mu Mata Sun fita za6en sannan zaici ko?. Kuma munga mara Kunyar da zai Kuma campaign din wannan Mutumin mara Kishin Alummar sa.