Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nada Zahara’u Nasir Ahmed babban mataimaki ta musamman kan harkokin yada labaran radio da Tv na musamman nan take.
Nadin nata a cewar gwamnan, ya biyo bayan nazari sosai kan irin dimbin gogewar da ta samu a aikin yada labarai, “… tare da la’akari da kokarinta na ganin ta samu kwarewa ta kowane fanni,” inji Ganduje.
“Ina taya ki murnar samun wannan sabon mukamin na babbar mataimakiya ta musamman, ga gwamna, Ina fatan zaki yi amfani da kwarewar ki wajen sauke nauyin da aka dora miki,” in ji shi.

Nadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu Kuma ya aikowa kadaura24.
Bayan yi mata addu’ar samun nasara, Gwamna Ganduje ya umarce ta da ta yi aiki tukuru tare da haɗa kai da sauran mataimakan gwamnan a kafafen yada labarai domin samun nasarar aikin da aka dora mata.
Kafin wannan nadin nata Zahra’u Muhd Nasir ta yi aiki da gidan Radio Freedom a matsayin Mai aika musu labarai daga gidan gwamnatin jihar kano.