Daga Kamal Yahaya Zakaria
Dan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta Kano, NNPP, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, ya yi kira da a gaggauta kama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, tare da gurfanar da shi gaban kuliya bisa laifin tada zaune tsaye da kuma tunzura al’ummar jihar kano.
A cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP ya aikowa kadaura24, yace Abba Yusuf ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su gaggauta daukar mataki ta hanyar kame Abdullahi Abbas domin dakile tashe-tashen hankula a siyasar Kano da kuma kare rayuka da al’ummar jihar kano.
A cewar sanarwar, shugaban jam’iyyar APC na jihar kano yana goyon bayan duk wasu ta’addanci da ake yiwa al’ummar kano musamman magoya bayan jam’iyyar NNPP a fadin birnin kano.

NNPP ta yi zargin cewa dan Abdullahi Abbas ne ya kawo wasu muggan makamai yayin da ake zargin Rayyanu wani jami’in ‘yan sanda daga yankin Gwale yana ba su kariya domin su aikata wannan aika-aika.
Sai dai abin takaicin shi ne, duk da kokarin da sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya yi na magance ‘yan bangar siyasa, Amma duk da hakan sun zargi manyan baturen yan sandan Gwale da Mandawari na taimaka wa tare da nuna bangaranci da goyon bayan jam’iyyar APC .
Idan zaku iya tuna cewa wasu hadiman Abdullahi Abbas ne suka shirya makamantan irin wadannan hare-hare a ranar 12 ga watan Fabrairu, 2019 inda aka kona gidan Alhaji Abba Kabir Yusuf, kuma shugabancin rundunar ‘yan sandan jihar Kano a lokacin basu ɗauki wani mataki ba, lauyoyin mu har yanzu suna jiran sakamakon binciken, amma abin ya ci tura.
Mun yi imanin cewa rashin sauke nauyin da ya rataya a wuyan jami’an tsaro na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya, kare kai ya halatta a Musulunci da kuma dokokin Nijeriya kamar yadda sashe na 35,36,39 da 41 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada. gyara.
Don haka dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP yana neman a gaggauta kama shi, a bincike da gurfanar da Abdullahi Abbas, da dansa Sani Abdullahi Abbas da sauran wadanda ake zargi da hannu a hare-haren, da tsokana da kalaman batanci da tunzura al’umma da kuma sauran ta’addancin da ake tafkawa kan magoya bayanmu da al’ummar kano baki daya.