Za mu cire tallafin man fetur a 2023 – Gwamnatin tarayya

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

 

Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.

 

Hajiya Zainab ta bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da ta gudanar a Abuja babban birnin ƙasar bayan kammala taron tattalin arziki na ƙasa karo na 28.

 

Kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito cewa biyan tallafin kudin man fetur ya laƙume naira tiriliyan 2.565 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022.

 

Haka kuma a cikin kasafin kudinta, gwamnatin tarayya ta ƙiyasta kashe naira tiriliyan 3.3 wajen biyan tallafin man tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2023.

 

Ta ci gaba da cewa kuɗin tallafin man na kawo wa kasafin kudin giɓin da dole sai an ciwo bashi kafin cike shi.

Talla

“Ba kuɗi ne da muke da su a hannu ba, kudi ne da muke karɓo bashinsu domin biyan tallafin”, in ji ministar.

 

“Wasu ƙasashe sun fara biyan tallafi saboda annobar Korona, da batun yaƙin Ukraine, to amma suna amfani da kuɗaɗensu wajen biyan tallafin, to amma mu bashi muke karɓowa domin biyan tallafin, to kun ga duka biyu kenan, dan haka dole mu dakatar da shi”, in ji ministar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...