Daga Aisha Aliyu Umar
Aisha Humaira dai tana daya daga cikin jarumai mata da tauraruwarsu ke haskawa A masana’antar kannywood, Sai dai anga kokaci guda ta jingine harkar fina-finan ta koma karkashin Kamfanin Mawakin wato Dauda Kahutu Rarara.
Kafin komawarta karkashin Kamfanin Na Mawakin, A Baya Ana Yawan Ganinta da mai shirya fina-finan nan Abubakar Bashir Mai Shadda, Inda bayan auren na mai shadda Kwatsam sai akaga ta koma wajen mawaki Rarara.

Hakan tasa mutane suka fara zargin c kamar akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu da Rarara sakamakon yanda a koda yaushe ake ganin su tare, hakan tasa mutane da dama suke .
Sai dai a wata hira da akai da mawaki Rarara an tambaye shi :

“Shin Akwai Soyayya Ne TsakaninKa Da Jaruma Aisha Humaira?”
Mawaki Rarara yace shi da Aisha Humaira ba soyayya bace kawai akwai kyakyawar alakar ta aiki a tsakaninsu, amma yace ba laifi bane kowa ya fadi abun da yake tunani.
” Aisha Humaira Darakta ce a kamfani na Kuma ita ce ta uku a kamfanin don haka dole a rika ganinmu tare da ita, kuma in ma da soyayya a tsakaninmu nan gaba ai zata fito tunda ita soyayya ai bata buya”. Inji Rarara