Gobara ta tashi a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke Kano.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin wutar ba, to sai dai wani mai shago a kasuwar ya shaida wa BBC cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar
Kawo yanzu wutar na ci , yayin da jami’an kashe gobara ke kokarin shawo kan wutar.
Wani ɗan kasuwar, Jamilu Zubairu ya ce wutar ta faru ne da misalin ƙarfe 9 na safe.
Sai dai ya ce yanzu haka jami’an hukumar kashe gobara sun je su na ta ƙoƙarin kashe wutar.





