Za’a Sake Bude Allurar Rigakafin Corona Kashi na 1- Dr Faisal

Date:

Gwamnatin Tarayya za ta rufe bayar da kashi na biyu na Allurar rigakafin COVID-19 a ranar 25 ga Yuni, yayin da za’a sake fara kashi na 1 a yau.


 Babban Daraktan Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Kasa, NPHCDA, Dokta Faisal Shuiab ne ya bayyana haka a taron kara wa juna sani na mako-mako kan sabunta allurar rigakafin a Abuja.


 Idan za a iya tunawa, an rufe kashi na 1 na rigakafin COVID19 a hukumance a ranar 24 ga Mayu 2021 tare da Inda aka yiwa mutune 1,978,808 yayin da mutum 680,345 suka karɓi na biyu.


  A cewar Dakta Shuaib, sake bude kashi na 1 na rigakafin COVID19 ya biyo bayan bukatar da ‘yan Nijeriya suka gabatar na yin rigakafin, saboda haka duk wanda ya shekara 18 zuwa sama ba a yi masa rigakafin ba zai iya ziyartar wurin da ake yin rigakafin mafi kusa don ayi masa kashi na farko na allurar ta AstraZeneca.


 Babban Daraktan NPHCDA ya kuma shawarci duk wadanda suka karbi allurar a kalla makonni shida da suka gabata da su ziyarci wurin allurar da ke kusa da su don karbar na su da Kashi na biyu na Allurar kafin ranar 25 ga watan Yuni.


 Ya ce Najeriya za ta karbi allurai miliyan 3.92 na Oxford / Astrazeneca a karshen watan Yulin ko farkon watan Agusta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...