Sha’aban Sharada ya shirya baiwa Matasan N-Powar Gudunmawa

Date:

Sanarwa


Gidauniyar Hon Sha’aban Sharada da hadin gwiwar Fitilar Jama’a na sanar da Dubunnan Masan Jjhar Kano wadanda suka samu aikin koyarwa na Npower, da cewa gidauniyar ta tanadi na’u’rorin Daukar hoton yatsa wato (Biometric) domin tantance su, kamar yadda hukumar jin kai ta kasa ta umarci dukkanin wadanda suka nuna sha’awar shiga cikin shirin.


Kananan Hukumomin Kano Municipal, Tarauni, Dala, Nassarawa,Fagge,Gwale,Kumbotso, Ungogo,Dawakin Kudu, Minjibir Zasu hadu a Office din Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada Dake, Sharada, Kai da Kafa, kusa da Kwanar Freedom.
Daga ranar alhamis 17 ga watan nan zuwa 23 fa watan Yuni 2021 daga karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma.

Sai kananan hukumomin : Karaye, Rogo,Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Madobi, Garun-Malam da zasu hadu a Karaye special primary school, dake Kofar Fada, Karaye A tun daga ranar 20 ga watan yuni zuwa 23 ga watan Yuni, tin daga karfe 9 na sa Safe zuwa 6 na yamma.

Kananan Hukumomin : Bichi, Bagwai, Shanono,Tsanyawa,Kunchi, Makoda,Dambatta,Dawakin Tofa Da Tofa
Zasu hadu a Bichi computer centre kusa da FCET Bichi, A rana kun 20 ga watan yuni zuwa 23 ga watan, Daga karfe 9 na safe zuwa karfe 6 na yamma.

Sai Kananan Hukumomin : Gaya, Ajingi, Albasu, Wudil, Garko, Warawa, Gezawa da Gabasawa
Da suma zasu hadu a: multi purpose, Centre Gaya,Alkala quarters, kusa da Gidan Garkuwan Gaya.


A rana kun 20 ga watan yuni zuwa 23 ga watan yuni, Tin daga karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma.

Sai kuma Kananan Hukumomin: Rano,Bunkure,Kibiya,Takai,Sumail,Kura, Doguwa,Tudun Wada, Kiru da Bebeji.
Inda zasu hadu a ofishin Emancipation Network d da ke lamba 12 Amman Anu Plaza, Kusa da banjin UBA, dake garin kano,
A ranakun 20 zuwa 23 ga watan yuni, tin daga karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma.

Sanarwa daga Mai magana da yawun Sha’aban Faruk Malami Sharada a madadin Shugaban Fitilar Jama’ar Kano Khalifa Mustafa Dankade, a madadin Hon Shaaban sharada Foundation

75 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...