Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar kashe gobara ta jihar kano ta tabbatar da konewa akalla shaguna sama da guda 100 a kasuwar yan tumatur dake Badume a Kano.
” A ranar Juma’a da misalin karfe 03:30 na yamma wani mutum mai suna Ibrahim tsalha ya kirawo ofishin mu ya sanar da mu tashin wata gobara a kasuwar Badume dake karamar hukumar Bichi, hakan tasa jami’an hukumar mu na Bichi suka taso domin kashe gobarar”.
Jami’in hulda da jama’a na na hukumar kashe gobara ta jihar kano PFS Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.

Yace kafin isar jami’ansu wurin wutar ta kone shaguna sama da guda 100, tare Kuma da jikkata wasu mutane guda 3 maza biyu mace daya.
“Bayan mun fito da mutanen cikin mummuna yanayi daga bisa ni dukkanin sun rasu Kuma mun mika kawawwakin ga wani jami’in Rundunar yan sanda dake ofishin yan sanda na Bichi wato Isfecta Mukaila Inuwa” . Inji Saminu Yusuf
Sanarwar ta Kara da cewa kashe wutar ta tseratar da akalla shuguna 100, sannan Kuma har yanzu ana bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
Ya yi kira ga al’ummar jihar kano baki daya dasu rika kashe wutar lantarki tare da cire duk wani abun wuta daga jikinta a duk lokacin da suka gama amfani da ita.