Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ta ya Alhaji Ahmed. Ali zaki murna da Fari cikin zabensa a matsayin sultan na 24 na masarautar katsinan maradi dake jihar maradi a kasar jamhuriyayr Niger.
A Yau Asabar 5-12-2022 Yan majalisar sarki masu zaben sarki mutum biyar da Amincewar Gmamnatin kasar suka bayyana Alhaji Ahmed Ali zaki dan tsohon sarki mai rasuwa A matsayin sabon sarkin maradi na Ashirin da hudu (24).
Sakon ta’ya murna nada Ahmed zaki na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano a yau Asabar 5-11-2022.
Farfesa Gwarzo, wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ya bayyana nadin Ahmed Ali zaki a matsayin Sultan na katsinan maradi da cewa Abu ne wanda ya dace kuma ya cancanta.
“ A madadin iyalina, Jami’ar MAAUN, ina mika taya ga Sabon sarki Ahmed Ali zaki “ in ji Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta ya murna ga sultan na 24.
Farfesa Gwarzo wanda kuma shi ne shugaban kungiyar jami’o’i masu zaman kansu na Afrika (AAPU) ya yi amfani da wannan dama wajen Ta ya Al-ummar masarautar maradi da Gmamnatin Jihar tare da shugaban kasar jamhuriyyar Niger da daukacin Al-ummar kasar murna da farin cikin nada sabon sarkin kuma yayi addu’ar Allah ya taya shi riko.
Kadan daga cikin Tarihin. An Haifi Ahmed Ali zaki shekarar 1969 a Maradi yayi karatunsa na boko a Nijar da Faransa har zuwa jami’a fannin tattalin arziki da tanadi kafin ya Shiga aikin Banki, ya taba rike hukumar Samar da kayan Noma ta kasa Caima kafin ya koma dan kasuwa mai Zaman kansa.
Sabon sultan yana da mata guda da yaya hudu, ya gaji mahaifinsa maremawa Ali Zaki Wanda ya mulki Katsinar Maradi daga 1 ga Oktoban 2005 zuwa 24 ga Watan yunin 2021 kafin wannan matsayi na Sarkin Katsinar Maradi Ahmed Ali Zaki na rike da mukamin Dan Baskore da mahaifinsa Ali Zaki ya nada sa