Kano da wasu jihohin Nigeria zasu fuskanci hazo da kura – Nimet

Date:

Daga Khalifa Abdullahi Maikano

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta ce ana sa ran kura da hazo daga Nijar da Chadi za su shigo cikin kasar nan cikin sa’o’i 24 masu zuwa a wasu sassan jihohin arewacin kasar da ke nuna yiwuwar shigowar yanayin sanyi.

 

Sanarwar da hukumar ta fitar na nuni da cewa hazon kura za ta yi kamari ne a jihohin Maiduguri, Yobe, Katsina, Kano, Kaduna, Gombe, Bauchi da Jigawa, yayin da jihohin da ke shiyyar Arewa ta tsakiya za su fuskanci yanayi mai zafi da rana da kuma hazo.

Talla

Ana sa ran cewa wannan yanayin zai ci gaba har zuwa kwanaki 3 masu zuwa tare da karuwar  Yanayin.

Bisa al’ada a yanayin sanyi ana fuskantar hazo da kura da zafin rana wanda wani lokacin yakan haifar da ciwon sankarau, hukumar NiMet ta shawarci masu ababen hawa da suyi tuki cikin taka tsantsan da kuma duba lafiyar ababen hawansu a duk lokacinda zasuyi amfani dasu.

 

Har ila yau hukumar ta shawarci ma’aikatan kamfanin jirgin sama dasu samu rahotannin yanayi daga NiMet kafin gudanarda aiyukansu duba da yanayin sanyi da ake kokarin shiga

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...