An Dakatar da Sarkin Zurmi bisa zargin Haɗa Kai da Yan Bindiga

Date:

Daga khalifa Abdullahi Maikano

Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Mai Martaba Sarkin Zurmi a Jihar Zamfara, Alhaji Atiku Abubakar bisa zargin sa da hannu a karuwar hare-haren ‘yan bindiga a masarautarsa.


 Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren gwamnatin jihar Zamfara Alhaji Kabiru Balarabe Wadda kuma aka rabawa manema labarai a Gusau.


 Sanarwar ta ce, an kafa wani kwamiti na mutum 9 da zai binciki zargin a karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ibrahim Wakkala Muhammad da sauran manyan jami’an gwamnati ciki har da wakilan hukumomin tsaro.


 A cewar sanarwar, ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa a cikin makonni 3.


 A halin yanzu, Alhaju Bello Suleiman (Bunun kanwa) shine zai kula da lamuran masarautar da gaggawa

91 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya fidda wasu mata 8 daga gidan yari

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir ya biyawa wasu mata...

Barin jam’iyya bayan ka ci zabe a cikinta babban zunubi ne a Siyasa – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya...

Nigeria ka iya zama kamar China idan aka koma tsarin jam’iyya daya – Ganduje

  Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje...

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...