Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Date:

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar Kano ta ce tana nan kan bakarta na tabbatar da kare kadada 3000 da take kula da shi a dajin dansoshiya dake karamar hukumar Kiru a jihar Kano.

” Mun sami labarin wasu manoma da suka zargi jami’anmu dake aiki a wajen da karbar kudade a wajensu idan sun je share gonakinsu, to muna so duniya ta sani Wannan maganar ba gaskiya ba ce kitsa ta kawai aka yi don a bata sunan wannan rundunar ta mu”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar civil defense ta kasa reshen jihar Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Sanarwar ta ce hukumar NSCDC, ta jihar Kano tana so ta bayyana babu shakka cewa wannan labari karya ne, ba gaskiya ba ne, wasu ne daga yankin (Dansoshiya) suke son bata sunan hukumarsu.

“Muna so mu bayyana a fili cewa jami’anmu na civil defense dake aiki a yankin ba su taba karbar kudi ko wani abu daga manoma da sunan tara ko kuma kudin aikin gona ba. Sabanin haka ma su ne suka rika kokarin baiwa jami’anmu na goro a lokuta daban-daban, don a bar su su noma gonakin da ba na su ba, amma jami’an mu suka ƙi karba . Tun daga wancan lokacin ne wasu daga cikin su (manoma) da ba su ji dadi ba suka sha alwashin bata sunan hukumar amma muna sanar da su ba za su yi amfani ba”.

InShot 20250309 102403344

“Hukumar NSCDC a shirye take kuma ta kuduri aniyar ganin cewa babu wani nau’i na zarge-zarge da za su hana jami’an mu yin abin da ya kamata su yi; wato karewa da kiyaye hekta dubu uku (3000) na filin kiwo na Dansoshiya”. Inji sanarwar

Kuma mu na son duniya ta sani cewa akwai umarnin Kotu da ya hana yin duk wani abu da bai dacewa a cikin wancan fili, don haka rundunar za ta cigaba da kiyaye wancan fili mai fadin hekta 3,000 daga yin duk wani abu da ya saba ka’ida .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...