Kwamishinan Noma na Kano ya yabawa Buhari saboda da Karrama A A Rano da lambar girmamawa ta OON

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kwamishinan harkokin noma na jihar kano Dr Yusuf Jibril Rurum J Y ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ya zabo Shugaban rukunin kamfanonin A A Rano Nigeria Limited Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, Saboda karrama A A Rano da lambar girmamawa ta OON, sakamakon irin taimakon da yake yiwa al’umma Kasar nan baki daya.

 

Dr. Yusuf Jibril JY ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu Kuma aka aikowa kadaura24 a Kano.

 

“Babu shakka an yi amfani da chanchanta wajen zabo A A Rano domin bashi irin wannan lambar ta kasa wadda na yi Imani zata karawa Uban a wajena kwarin gwiwar cigaba da tallafawa rayuwar al’umma, domin shi ya yarda arzikin da Allah ya bashi, ya ba shi ne don ya tallafawa al’umma”. Inji kwamishinan Noma

Talla

 

Yace wannan karramawa da aka yiwa A A Rano ta tabbatar da cewa ba’a San rai ba wajen lalubo wadanda aka baiwa lambar girmamawar a wanann karon domin an baiwa dan kishin kasa mai jin tausayin mutane kuma wanda ya yarda a jingina da shi a tashi.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar talatar da ta gabata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika lambar girmamawa ta OON ga Alhaji Auwalu Abdullahi Rano wanda hakan ce nuna cewa daga jiya talata dole ne a ƙarshen sunan A A Rano a Saka masa OON domin tabbatar da karramawar da shugaban kasa ya yi masa.

Talla

Kwamishinan harkokin noma na jihar kano Dr. Yusuf Jibril Rurum J Y yace a madadin sa da iyalansa da yan uwan da abokan arziki da al’ummar yankin kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure yana taya Alhaji Auwalu Abdullahi Rano OON murnar samun Wannan karramawa da shugaban tarayyar Nigeria ya bashi.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar samarin Tijjaniyya ta yi Allah – wadai da hukuncin Kotun ECOWAS

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Kungiyar Samarin Tijjaniya ta kasa tace...

Majalisar dokokin Kano da Freedom Radio sun fara musayar kalamai

Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi al'ummar jihar Kano...

2027: Shugabannin APC a Kano ta Kudu sun mika bukatarsu ga Sanata Kawu Sumaila

Shuwagabannin jam’iyyar APC da Sakatarorin su na mazabar Kano...

Tinubu ya sake ƙaddamar da aiki titin Abuja zuwa Kaduna

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gina...