Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 30 a Benue

Date:

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani harin ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Agatu da ke jihar Benue a tsakiyar Najeriya ya kai kusan 30, yayin da har kawo yanzu ake tsammanin samun ƙarin wasu gawarwaki.

Mutane da dama sun ƙaurace wa garin da aka kai harin saboda fargabar abun da ka je ya zo, la’akari da yadda ake yawan samun hare-haren ramuwar gayya a ƙaramar hukumar.

Mahukunta sun ce ana ci gaba da neman masu hannu a harin don daukar matakin doka a kansu.

Bayanai na cewa an kai harin ne kan kasuwar garin Odugbeho da yammacin ranar Lahadi, yayin da ake tsaka da cin kasuwar, kwatsam sai maharan suka fara bude wuta kan mai uwa da wabi, abun da ya sa jama’a fara gudun tsira da rai.

Wasu rahotanni dai na cewa maharan da suka addabi kananan hukumomin Guma da Makurdi da kuma Agatun da aka kai harin yanzu kan fito ne daga jihar Nassarawa da ke makwabtaka da Benue, su ƙaddamar da hare-hare su kuma sake komawa inda suka fito.

Wasu mutane da ke wasan ƙwallon ƙafa a wani filin bal da ke kusa da kasuwar garin na Odugbeho na cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, kamar yadda shugaban karamar Agatu Adoyi Sule ya shaida wa BBC.

Cathrine Anene, ita ce mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar ta Benue, ta kuma shaida min cewa an sanar da su a lokacin da maharan suka isa garin.

Karamar hukumar ta Agatu dai na cikin kananan hukumomin jihar Benue da suka fi fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga a jihar Benue, ga kuma rikicin manoma da makiyaya da ake fama da shi a yankin.

Wata majiya da ba ta yarda a ambaci sunanta ba, ta ce hatta harin na ranar Lahadi, akwai alamun cewa na ramuwar gayya ne da wani bangare ya gayyato dan uwansa, don kai wa abokan tsamar su hari, saboda yawan sabanin da ake samu tsakaninsu a baya-bayan nan.

Wasu majiyoyi sun ce akwai yiwuwar samun ƙarin wasu gawarwaki yayin da ake ci gaba da bincike.

69 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...