Nafi kowanne dan takarar majalisar tarayya a Nasarawa chanchanta – Aminu Ala

Date:

Daga Abdulhamid Durimin iya
Shahararren mawakin nan Alhaji Aminudden ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waka, wanda Kuma shi ne dan takarar majalisar tarayya a Nasarawa a jam’iyyar ADP yace duk cikin yar takarar majalisar tarayya a karamar hukumar Nasarawa yafi kowannen su chanchanta .
Aminudden ladan Ala ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Kano.
Alan waka yace a batun wakilcin al’umma ana bukatar mutumin da yake da yasan matsalolin al’umma Kuma yasan hanyoyin da zai bi wajen magance matsalolin Kuma ni nasani.
” Da kake maganar ana yamutsa hazo saboda Sha’aban Ibrahim Sharada ya bani takarar majalisar tarayya, to kake da shi a Nasarawa wanda ya fini chanchanta, kuma baya bukatar a tallata shi, wanda za’a iya nuna shi a matsayin Dan takara kuma ya chanchanta kamata”.
Talla
” A abatu takarar ana bukatar mutum Mai mutunci, mutum shahararre, mutum mai karrama mutane, ana da bukatar mutumin da shekarunsa suka kai kuma mutum mai Ilimi dai-dai gwargwado, Kuma al’umma suka San shi, to sai ka duba duk cikin Yan takarar da ake da su a Nasarawa waye wanda zai baiwa Sha’aban abun da yake bukata idan ba ni ba”. A cewa Alan waka
Ya ce ya kamata mutane su sani sun dade suna bada gudunmawa a Siyasa ta hanyar wayar da akan mutane su zabi shugabanni da wakilai na gari, don haka yace suka ga dacewar a wannan karon suma su fito su gwada damar da kundin tsarin mulki kasa ya basu da kuma basirar da suke da ita.
Alan waka yace ya yi tanadi na abubuwan da zasu taimaka wajen ciyar da al’ummar Nasarawa gaba fiye da yadda suka Saba gani a baya.
Talla
” Zan bada gudunmawa sosai don bunkasa Ilimi saboda sai da Ilimi mutum zai san waye shi, na yi tanadin bada horo da kuma bada tallafi ga Masu kananan masana’antu da ma wadanda basu da sana’o’in da suke don dogaro da kai da dai sauransu “. A cewar ala
Aminudden ladan Abubakar ya yi fatan al’ummar karamar hukumar Nasarawa da jihar kano baki daya zasu cigaba da mara baya ga Dan takarar gwamna Sha’aban Sharada da sauran yan takarar kujeru daban-daban don Samun nasarar jam’iyyar ADP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...